✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan Najeriya miliyan biyu ne za su amfana da tallafin ‘Survival funds’ – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce akalla ‘yan Najeriya miliyan daya da dubu 700 zuwa miliyan biyu ne ake sa ran za su…

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce akalla ‘yan Najeriya miliyan daya da dubu 700 zuwa miliyan biyu ne ake sa ran za su ci gajiyar tallafin kudade na gwamnatin tarayya karkashin shirin ‘Survival Funds’ da ma wasu shirye-shiryen.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi a taron tattaunawar da wata mujalla mai suna Africa Reporters ta shirya ta fasahar bidiyo.

Taron dai ya mayar da hankali ne kan tsare-tsaren tattalin arzikin da Najeriya ta shirya bayan farfadowa daga cutar COVID-19.

Mataimakin shugaban ya ce a karkashin shirin da gwamnatin ta bude a kwanan nan, ‘yan Najeriya da kuma kanana da matsakaitan sana’o’i da dama ne za su ci alfanun tallafin da yawansa ya kai Naira biliyan 60.

Osinbajo ya bayyana nasarar da aka samu cikin kwanaki uku da fara rijistar shirin a matsayin mai karfafa gwiwa, yana mai jaddada manufar gwamnatinsu na tabbatar da yin komai a bude yayin zabar wadanda za su amfana.

Kazalika, Osinbajo ya ce yanzu haka akwai kimanin manoma miliyan biyu da aka tantance za su ci moriyar bayar da tallafin noma.

Ya ce shirin zai samar da aikin yi da kuma tabbatar da samarwa kasa da wadataccen abinci.

Ya ce tuni gwamnatin ta samar da Naira biliyan 500 daga cikin Naira tiriliyan 2.3 da aka ware a cikin kasafin kudin bana domin aiwatar da shirin inda ya ce cikason kuma za a samo ne daga rancen da Babban Bankin Kasa na CBN zai bayar.