✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya na ji a jikinsu a mulkin Buhari —Obasanjo

Osabasanjo ya ce Najeriya ta gaza a karkashin mulkin Najeriya

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun ya ce Najeriya ta gaza a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Obasanjo ya ce Najeriya na bukatar dauki daga sukurkucewar da ta yi kuma ya zama wajibi a kawo  mata dauki kafin ta balbalce.

Ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar makala mai taken ‘Ceton Najeriya daga sukurkucewa’, a wani taro da kungiyoyi da dama daga sassan kasar suka halarta a Abuja a ranar Alhamis.

A cewar Obasanjo Najeriya ba ta taba samun kanta cikin rarrabuwar kai kamar yanzu ba, sannan ya dora laifin a kan gwamnati mai.

“Na ji dadi da a yanzu kowa ke ji ajikinsa, domin duk dan Najeriya a yanzu yana ji a jikinsa.

“Yanzu talauci ya yi wa jama’a katutu, tattalin arzikin kasa na cikin mawuyacin hali, Najeriya na cikin halin gargara ta yadda in ba an kai mata dauki ba za ta sukurkuce”, inji shi.

Ya ce masu fatan a raba kasar su sani cewa ko da hakan ta faru bangarorin za su ci gaba da zama a matsayinsu na makwabtan juna, za kuma su ci gaba da mu’amala kamar yadda suka saba.

Tsohon shugban kasar ya dole idan za a magance matsalolin Najeriya a fara da magance matsalar rarrabuwar kai a tsakanin al’umma, domin babu kasar da za ta ci gaba idan al’ummarta suka rarraba

A karshe Obasanjo ya yi kira ga mahalarta taron da su hada kansu domin ciyar da kasar gaba.

Kungiyoyin da suka halarci taron sun hadar da kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere da Kungiyar Dattawan Arewa da ta Ohanaez ta al’ummar Ibo da kungiyar mutanen yankin Neja Delta.