✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya na nuna halin ko-in-kula da COVID-19 – NCDC

NCDC ta ce akwai barazanar cutar na iya dawowa muddin aka ci gaba da zama kara zube.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce Najeriya na fuskantar barazanar koma-baya a nasarar da take samu wajen yaki da COVID-19 saboda halayyar ’yan kasar da dama a kan cutar yanzu.

Hukumar ta yi zargin cewa mutane da dama yanzu na nuna halin ko-in-kula da kuma yin buris da matakan kariya daga cutar, tamkar ma yanzu babu ita.

Babban Daraktan hukumar, dakta Chikwe Iheakweazu ne ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabin Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da COVID-19 karo na farko a Abuja ranar Litinin.

Ya ce hakan na da matukar illa saboda akwai barazanar cutar na iya sake dawowa muddin aka ci gaba da zama kara zube.

Ya ce, “Cutar COVID-19 bata tafi ba. Ina kira ga ’yan Najeriya da su yi wa Allah su kare kansu kuma su kare kasarmu.

“Gwajin kafin, da kuma bayan an dawo daga tafiya da kuma killace kai na da matukar muhimmanci. Ya zama zama wajibi mu yi hakan don kaucewa daukar tsuraran matakai da za su iya yin mummunar illa ga tattalin arzikinmu.

“A yanzu haka akwai matakai da yawa da muka dauka wadanda a farkon annobar babu su,” inji shugaban na NCDC.