✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya na shan wuya —Jega

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Attahiru Jega da tsohon Shugaban Cocin Katolika na Abuja, John Cardinal Onaiyekan, sun shaida wa Shugaba Buhari cewa…

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Attahiru Jega da tsohon Shugaban Cocin Katolika na Abuja, John Cardinal Onaiyekan, sun shaida wa Shugaba Buhari cewa ’yan Najeriya na cikin bala’in rashin tsaro da annobar COVID-19.

Sun bukace shi ya gaggauta daukar duk wani matakin samar da tsaro a kasar ko da zai kai ga korar Manyan Hafsashin Tsaron Kasar ne.

Dattijan sun bayyana hakan ne a sanarwa da suka fitar ranar Lahadi mai taken: “Shugaban Kasa da Gwamnoni yanzu ne lokacin tattaunawar sasanci”, a madadin Kungiyar Zaman Lafiya da Ingantacciyar Gwamnati (Nigeria Working Group on Peace-building and Governance).

Kungiyar ta yi nuni da bincike da hukumar USIP Commission ta gudanar da ke alakanta annobar COVID-19 da rashin kwanciyar hankali da rikice-rikicen da ke faruwa a kasar nan.

Sun kuma ba gwamnati shawarar hanyoyin da za ta bi don magance matsalolin annobar da rikice-rikicen da take fama da su.

“A kullum garkuwa da mutane karuwa yake yi, ’yan Boko Haram na ci gaba da ta’addanci, ga ’yan gudun hijira ko ina da kuma ’yan bindiga a Arewa maso Yamma.

“Ta’addanci a kauyuka ya hana manoma zuwa gonaki saboda tsoron kar a kashe su, wanda hakan barazana ce ga yanayin abincin kasa”.

Da haka suka bukaci Shugaban Kasar ya gaggauta daukar matakin tattaunawar sasanci domin magance matsalolin da suka dabaibaye kasar.

Sun kuma yi kira ga tsoffin shugabanin kasa da su zauna domin bullo da hanyar sasanci da gwamnoni za su tabbatar an aiwatar tun daga jihohi har zuwa kauyuka.

Game da rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da farraka kabilu, sun koka cewa har yanzu kadan daga cikin masu laifin aka hukunta.

Da hakan suka bayar da shawarar a kara gudanar da binciken kan wasu manya-manyan rikice-rikicen manoma da makiyaya da aka samu.

Sun kuma yi kira da a sauke hafsoshin tsaron masu ci idan har hakan zai kawo zaman lafiya a Najeriya.