✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya su daina karbar tsofaffin takardun kudi a bankuna —CBN

A gaggauta kai korafin bankunan da ke ci gaba da bai wa jama'a tsofaffin takardun kudaden.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya umarci jama’ar kasar nan da su daina karbar tsofaffin takardun kudaden da bankunan kasuwanci ke bayarwa, saboda ganin lokacin daina amfani da su na kara karatowa.

Mataimakiyar Daraktan Sarrafa Kudaden bankin, Dokta Rekiyat Yusuf ce ta bayyana haka lokacin da take fadakar da ‘yan kasuwa a birnin Lokoja dangane da sabunta takardun kudin da bankin ya yi.

Ta ce, bankin ya tanadi hukunci mai tsauri a kan bankunan kasuwancin da aka samu na ci gaba da bai wa jama’a tsofaffin takardun kudaden wadanda za a daina amfani da su daga ranar 31 ga watan Janairu 2023.

Daraktar ta bukaci jama’a da su gabatar da korafi a kan duk wani bankin kasuwancin da ya ci gaba da bai wa mutane tsofaffin takardun kudaden ta na’urar ATM, yayin da ta bukace su da gaggauta kai tsofaffin kudaden bankin domin sauya musu da sabbi.

Kazalika ta ce babu dalilin da bankunan za su ci gaba da bai wa jama’a tsofaffin takardun kudaden domin Babban Bankin ya yi tanadi na musamman wajen wadata su da sabbin kudaden da aka buga.

Ta yi bayani a kan dalilan da bankin ta sabunta kudaden da suka hada da dakile ayyukan ta’addanci da ayyukan masu garkuwa da mutane da cin hanci a tsakanin al’umma da kuma magance hauhawar farashin kayan masarufi.

Sai da mutane na ci gaba da korafi kan yadda sabbin takardun kudaden ke ci gaba da karanci a hannun mutane.