✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya sun koka da karancin sababbin takardun kudi a bankuna

Daga ranar 31 ga watan Janairu tsofaffin takardun kudin za su daina aiki.

’Yan Najeriya sun koka kan yadda sababbin takardun kudi ke wuyar gani bayan kwanaki 17 da fara amfani da su a hukumance.

Aminiya ta zanta da wasu al’ummomi a Jihar Kano da Birnin Tarayya Abuja, inda suka ce har yau ba su taba sanya su a idonsu ba ma balle su rike a hannunsu.

A Jihar Kano, wani dan kasuwa a Singa mai suna Audun Ghali, ya ce wajen sau 10 yana zuwa ATM amma ko sisin kwabo bai gani ba na sabon kudi.

“Wurin da kadai za ka iya samun sabon kudin sai banki, shi ma sai idan kudin da za ka cira da yawa, ko ka san ma’aikatan”, in ji shi.

Sai dai wani mai suna Alhaji Nuhu Danliti ya ce, ya samu sababbin takardun kudin, amma kashi biyu na adadin duka kudin da ya cira a bankin kadai ya samu.

“Ba iya ni kadai ba ne, abokina ma da ya cire N1m, sai N300,000 ya samu sababbi.

“Wannan ne ma kadai lokacin da na taba ganin sabon kudi, kuma abin takaici ma ba su da inganci, shi ya sa abokan huldarmu ba sa karbarsu.

Daga Birnin Tarayya Abuja ma haka batun yake, domin a ziyarar da Aminiya ta kai Bankin GT da Zenith da ke unguwar Jabi, babu wanda a ciki ke bayar da sababbin kudin.

Jami’in da ke gadin Bankin GT dai ya sanar da wakilinmu cewa, har yau ba su taba zuba sababbin takardun kudi a injinan ATM din ba.

Wani  mai suna Philip Abu ya shaida wa wakilinmu cewa, duk da wa’adin da gwamnati ta dibar wa tsofaffin kudin bai cika ba, mutane kan je bankin su tayar da hayaniyar sai an basu sababbin.

“Abinda suke iya yi maka shi ne su baka N1,000 guda daya rak, don sun ce N500 da N200 sun kare tas”, in ji Philip.

Sai dai Aminiya ba ta yi nasara ba a kokarin jin ta bakin Babban Bankin Najeriya (CBN), domin Kakakinsa, Osita Nwanisobi, bai yi martani ba, watakila saboda hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

Gwamnatin Tarayya dai ta ce daga ranar 31 ga watan Janairu, tsofaffin takardun kudi na N200, da N500 da N1,000 za su daina aiki.

Daga Simon E. Sunday da Faruk Shuaibu (Abuja) da Zahraddeen Y. Shuaibu da Rahima Shehu Dokaji (Kano).