✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya za su yi kewar Buhari idan ya sauka daga mulki —Garba Shehu

Za a rika yabon Buhari kamar yadda a yanzu ake yabon Goodluck Jonathan.

’Yan Najeriya za su yi kewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da zarar wa’adin mulkinsa ya kare.

Babban mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan kafafen yada labarai, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shirin Sunrise Daily na Channels TV a ranar Litinin.

Mallam Garba ya koka kan irin caccakar da ake yi wa shugaban kasar, yana mai cewa duk wani shugaba irin haka ke faruwa da shi amma da zarar ya kammala wa’adi sai a koma yabonsa.

Ya ce ba a nuna kauna ga shugabanni a lokacin da suke mulki.

Ya bayar da misali da zamanin mulkin Goodluck Jonathan wanda ya ce mutane sun yi ta sukarsa amma a yanzu, ya zama mutumin da ’yan Najeriya da dama ke yabo.

Mallam Garba Shehu ya ce irin haka za ta faru idan Buhari ya mika mulki ga Shugaban Kasa na gaba.

Game da manufar takaita amfani da garin kudi, Garba Shehu ya ce tsarin na gwamnati mai ci abin so ne a don haka ba za a soke shi ba.

A cewarsa, “takaita amfani da takardun kudi ci gaba ne ga ’yan Najeriya saboda kasashen da suka ci gaba tuni suke tafiya a kan wannan tsarin.”

Al’ummar Najeriya sun yi ta fuskantar matsaloli saboda karancin takardun kudi tun bayan da gwamnati ta bijiro da tsarin sauya fasalin takardun kudin.