✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sa-kai sun aika ’yan bindiga lahira a Kasuwar Dansadau

Wasu ’yan bindigar sun fake a cikin shaguna da gidaje da ofishin ’yan sanda domin samun tsira

’Yan sa-kai a Jihar Zamfara sun yi wa ’yan bindiga kofar rago a kasuwa tare da aika da dama daga cikinsu lahira a Dansadau.

A ranar Juma’a ne ’yan sa-kan, yawancinsu daga Ruwan Tofa da wasu al’ummomi makwabta, suka yi wa kasuwar tsinke suka kashe wadanda ake zargi ’yan bindiga ne.

Ana ganin matakin ’yan sa-kan daukar fansa ne a kan harin da ’yan bindiga suka kai wa Ruwan Tofa a ranar Alhamis.

Shaidu sun ce samamen ’yan sa-kan a kasuwar ta dabbobi da hatsi ya sa mutane tserewa saboda gudun martani daga ’yan bindiga.

“Yanzu ina cikin gida, gawarwarkin wadanda ake zargi da ayyukan ’yan bindiga na kwakkwance a cikin kasuwa. Mutane na cikin zullumin abin da zai iya biyo baya.

“Da farko ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa Dansadau, wanda ya tilasta mutane fasa tafiye-tafiye. Direbobin motocin haya suna yajin aiki saboda yawan fashin ’yan bindiga a kan hanyar.

“Da ’yan sa-kai suka zo, sai da suka tare duk wata hanyar fita ko shiga kauyen, sannan sauran suka tafi bangaren sayar da dabbobi a kasuwar suka karkashe mutanen,” inji wani mazaunin garin Dansadau.

Shi ma wani dan garin ya ce, “Wasu ’yan bindigar da suka ga alamar matsala, sun tsere zuwa cikin shaguna da gidaje da ofishin ’yan sanda suka buya. Gaskiya abun ya tayar mana da hankali.

“Yanzu dai jami’an tsaro na yin sintiri a kan tituna domin magance yiwuwar karya doka da oda,” inji shi.

Mun kasa samun kakakin ’yan sanda na Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ko zai yi mana karin bayani.

Kwamishinan Tsaro da Harkoki Cikin Gida na Jihar kuma, Abubakar Dauran bai amsa kiran rubutaccen sakon da muka yi masa ba.