✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sa kai sun kashe liman yana sallah da wasu mutum 10 a Sakkwato

’Yan sa kai sun yi wa kasuwar Mammade dirar mikiya suna bin Fulani suna harbewa.

Akalla mutum 11 ne ’yan haramtacciyar kungiyar nan ta sa kai suka kashe a kasuwar kauyen Mammande da ke Karamar Hukumar Gwadabawa a Jihar Sakkwato.

Daga cikin mutanen da ’yan sa kan suka bude wa wuta har da wani limami a garin Salame a lokacin da yake taska da sallah a kauyen na Mammade.

’Yan sa kan sun yi wa kasuwar dirar mikiya ne dab da la’asar, a lokacin da kasuwar ta cika makil, ana ta hadahada, suka rika tsintar Fulani suna harbin su.

“Sha daya daga cikinsu (Fulani) suka mutu nan take, hudu suka samu munanan raunuka a hannu a wurin kare harbin bindiga da aka yi masu.

“A maganar da nake yi da kai, mun kai wadanda suka samu rauni a asibitin kashi na Wamakko, gawarwakin kuma mun kai su dakin ajiye matattu na jiha”, da ke Asibitin Kwararru na Sakkwato, a cewar Shugaban Karamar Hukumar.

Ya ce lamarin da ya faru a ranar Alhamis ya zo da ba-zata, inda ’yan sa kai suka harbi Fulani 15 kai tsaye da bindigar toka, harba ka tsere.

A cewarsa, Fulanin sun zo ne kasuwar domin sayen kayan abinci da sauran abubuwa ne daga makwabtan kauyukkansu.

Ya kuma yi zargin cewa ’yan sa kai din sun kawo harin ne daga makwabtansu, Goronyo, amma dai bai tabbata ba ko a garin suke ba.

Sai dai ya bayyana cewa an kasa kama ’yan sa kan saboda makaman da suke rike da su.

Gwamnatin Jiha Sakwkato ta soke ayyukkan sa kai saboda yadda suke wuce gona da iri da kuma daukar doka a hannunsu.

Har yanzu ba a san dalilin harin ba, amma wasu na danganta shi da yawan hare-haren da ’yan bindiga, wadanda yawancinsu Fulani ne, ke kai wa a Jihar Sakkwato.

Wani Bafulatani da ya zanta da wakilinmu a Jihar Sakkwato ya bayyana harin a matsayin jahilci da rashin sanin ya kamata.

Duk yunkurin jin ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, bai yi nasara ba, har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.