✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sa-kai sun kashe masu kai wa ’yan bindiga bayanai 11 a Zamfara

An yi dauki ba dadi kafin ’yan sa-kai su yi nasarar cafke su sannan suka kashe su.

’Yan banga da aka fi sani da ’yan-sa-kai sun kashe wasu mutum bakwai da ake zargi suna kai wa ’yan bindiga bayanai a yankin Gada na Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.

Har wa yau, ’yan sa kai sun aika wasu mutum hudu lahira a yankin Kaura na Karamar Hukumar Namoda ta jihar, bayan sun rutsa wadanda ake zargin a Kasuwar Waya da ke garin Kaura Namoda.

’Yan sa-kai dai sun shafe tsawon lokaci suna neman mutanen ruwa a jallo kafin daga karshe su yi arba da su, su aika su lahira.

A yayin artabun, hakimin yankin da wasu mutum biyar sun rasa rayukansu, aka kuma sace mutane da dama, ciki har mata da kananan yara.

Tun da farko sai da ’yan sa-kan suka kai samame kauyen Tuskudu mai nisan kilomita daya da garin Gada suna neman wani mai kai wa ’yan bindiga bayanai.

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa wakilinmu cewa, “Daga cikin wadanda aka kashe akwai wata mata da mijinta da ’ya’yanta biyu.”

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce ba shi da masaniya game da faruwar lamarin, amma ya yi alkawarin yi mana karin haske da zarar ya samu cikakken bayani.

An jima dai ana takun saka tsakanin masu kai wa ’yan bindiga bayanai da kuma ’yan sa-kai a Jihar Zamfara, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama, wadanda ba su ji, ba su gani ba.