✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sa-kai sun kashe mutum 9 a kauyukan Fulani a Neja

“Na rasa mutum bakwai a dangina, nima da ba dan na gudu ba, da sun kashe ni.”

Akalla mutum tara ne rahotanni suka tabbatar da an kashe, wasu takwas kuma suka bace bayan wani harin da ake zargin ’yan sa-kain kauyen Maza-Kuka ne suka kai a Jihar Neja.

Sun kai harin ne, wanda ake zargin harin na ranuwar gayya ne, a kauyukan Fulani na Adogon Mallam da Gawun, a Karamar Hukumar Mashegu, tsakanin ranakun Lahadi da Litinin.

Aminiya ta gano cewa ’yan sa-kan sun kutsa kai kauyukan ne bisa zargin sune suka kai harin garin Maza-Kuka a kwanakin baya.

A harin na Maza-Kuka dai a lokacin, wanda aka kai masallaci lokacin da mutane ke sallar Asuba, an kashe mutum 18 sannan aka yi garkuwa da wasu 13.

Daya daga cikin mazauna yankin, Shehu Mohammadu na kauyen Gawun ya shaida wa wakilinmu cewa, “’Yan sa-kai sun zo kauyenmu, sun kona mana dakuna sannan suka gudu.

“An kashe matar kanina, Hauwa’u da danta mai wata 10.

“Sun kuma kashe dan kanina mai shekara uku da ’yarsa mai shekara 10, sun kuma kashe kanina, Aliyu da dana Muhammadu mai shekara 30.

“Na rasa mutum bakwai a dangina, nima da ba dan na gudu ba, da sun kashe ni,” inji shi.

Ya kuma ce sun yi awon gaba da shanunsa guda 51 da raguna 63 da awaki 53 da kuma babur, yayin da kannensa Abdullahi da Ali kuma aka kwashe musu awaki 38 yayin harin.

Shehu ya ce yanzu haka sun yi nesa da garin kuma ba zai koma ba saboda tsoron kada a kashe shi, yayin da wasu daga cikin ’yan uwansa suka gudu Kontagora.

Shi ma wani mazaunin yankin, Muhammad Marike ya ce yanzu haka ya gudu wajen Jihar ta Neja gaba daya.

A cewarsa “Bayan harin na ranar Litinin din makon jiya da ya kai ga kashe Dagacin garin da kaninsa, sun sake dawowa ranar Laraba inda suka dirar mana. Nima sa’a na ci daya daga cikin ’yan sa-kan ya san ni, ya ce a kyale ni. Yadda na samu na tsira kenan.

“Sun gudu da mutum takwas, kuma har yanzu babu wanda ya san inda suke. Wasu daga cikin mutanenmu sun gudu Jebba, wasu Zariya, wasu ma Kano,” inji Muhammad.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce tuni rundunarsu ta girke jami’ai na musamman a yankin don farautar masu hannu a cikin harin.

Ya ce tuni suka kwantar da tarzoma a yankin, yana mai kira ga mazauna kauyukan da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kama maharan.

Aminiya ta gano cewa yayin jerin hare-haren, hatta mata da kananan yara ba a bari ba.