✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda ba sa bukatar karin wata makaranta

Rundunar ’Yan sanda ta Kasa ta sanar a ranar Talata 4, ga Fabrairun bana, cewa ta kaddamar da wata sabuwar makaranta ta jami’an ’yan sanda…

Rundunar ’Yan sanda ta Kasa ta sanar a ranar Talata 4, ga Fabrairun bana, cewa ta kaddamar da wata sabuwar makaranta ta jami’an ’yan sanda mai suna National Institute for Police Studies.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, Frank Mba, ya fada a cikin sanarwar cewa samar da wannan makaranta wani yunkuri ne da rundunar ke yi wajen ganin ta samar da kwararrun jami’an ’yan sanda da za su taimaka wajen tabbatar da tasro a  kasar nan.

Mba, ya ci gaba da cewa makarantar za ta hada gwiwa da masana da jami’an tsaro da ’yan sandan duniya da sauran jama’a don samar da ingantaccen bincike kan sha’anin tsaro.

Ya ce makarantar wacce za ta yi aiki kafada-da-kafada da Kwalejin Kananan Hafsoshin ’Yan sanda ta Wudil da ke Jihar Kano za ta rika yaye kwararrun jami’an ’yan sanda da kuma wadansu jami’an tsaro da suke bukatar horo da kwarewa wajen tabbatar da tsaron al’umma. Haka kuma makarantar za ta rika tattara bayanai da kuma horar da manyan jami’an ’yan sanda da suka kai mukamin kwamishina.

Mba ya ce tuni an zabi wani Farfesa kan harkokin ’yan sanda kuma Mai ba Babban Sufeto ’Yan sandan Kasa Shawara, Olu Ogunsaki, a matsayin Daraktan makatantar wacce za ta fara aikin wucin-gadi a harabar Makarantar ’Yan sanda ta Jos a Jihar Filato.

Kakakin ya ce Sufeto Janar na ’Yan sandan ya bayyana cewa samar da wannan makaranta zai taimaka wajen horar da manyan jami’an ’yan sanda sababbin hanyoyin tunkarar barazanar tsaro da kasar nan take fuskanta.

Samar da makarantar da za ta rika horar da manyan jami’an tsaro game da harkokin tsaro abu ne mai kyau, musamman ganin yadda kasar nan take fuskantar matsalar tsaro a yanzu.

Amma duk haka, a halin yanzu, mun lura cewa akwai wani sabon yayi gasar kafa makarantu a tsakanin hukumomin tsaro daban-daban. Sojan kasa da sojan sama da sojan ruwa duk sun kaddamar da jami’o’insu da kuma wasu makarantu na horarwa wadanda ake sa ran za su bayar da gudunmawa wajen kawo karshen matsalar tsaro.

Wannan fa kari ne a kan wadanda ake da su kamar Kwalejin Koyar da Dabarun Yaki ta Kasa da kuma sauran kwalejojin horar da manyan ma’aikatan tsaro da ake da su a kasar nan wadanda suke bayar da gudunmawa wajen horar da jami’an tsaron.

Lura da yadda kasar nan take fama da matsalar tattalin arziki a yanzu, bai dace ba a ce an kirkiro da wata hanya wacce za a salwantar da dan abin da kasar take riritawa. Abin da muke sa ran hukumomin ’yan sanda su yi a yanzu shi ne su mayar da hankali kacokan kan bayar da horo da kuma samar da ’yan sanda da za su iya tunkarar matsalar tsaron da kasar nan take ciki a yanzu. Haka kuma muna sa ran mu ga hukumonin na ’yan sanda sun mayar da hankali kan samar da kayan aiki da dabarun aiki na zamani ga jami’ansu.

Amma a bin mamaki ne ganin cewa Rundunar ’Yan sandan ba ta ma da niyyar daukar karin sabbabin jami’ai, kai abin haushi ma rabon da a dauki sababbin jami’ai masu yawa tun kimanin shekara uku da suka wuce. Domin yunkurin da ta yi na daukar sababbin jami’ai a ’yan kwanakin nan ya ci karo da kalubalen rashin fahimta a tsakanin Shugaban ’Yan sandan Najeriya da Hukumar Harkokin ’Yan sanda ta Kasa.

Mun hakikance cewa hukumomin ’yan sanda za su iya samar wa manyan jami’ansu cikakken horo  ta wasu hanyoyi amma ba ta wannan hanya ta samar da wata sabuwar makaranta da ba a bukatarta a yanzu ba, wacce kuma za ta lashe makudan kudi da gwamnati za ta iya amfani da su don aiwatar da wasu muhimman ayyuka.

Don haka muna da yakinin cewa kamata ya yi hukumomin ’yan sandan su zuba kudin da suka yi niyyar amfani da su wajen gina wannan makaranta wajen sawo wa jami’ansu kayan aiki da kuma daukar sababbin jami’ai da za su taimaka wajen kawo karshen matsalolin tsaro da kasar nan take fuskanta.