✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda na neman mutum biyar ruwa a jallo a Zamfara

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara na neman wasu mutum biyar ruwa a jallo bisa zargin kisan gilla da aka yi wa wani likita a garin…

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara na neman wasu mutum biyar ruwa a jallo bisa zargin kisan gilla da aka yi wa wani likita a garin Gusau.

’Yan bindiga sun kutsa gidan Dakta Enoch Okoara da ke a unguwar Mareri, a kwanakin baya, inda suka nemi ya ba su kudi amma ya ki, su kuma suka kashe shi ta hanyar sara da adda suka kuma cinna wa gawarsa wuta.

“Muna neman sauran kuma za mu kama su don tabbatar ba su guje wa shari’a ba. Idan mun kama su kuma muka gama bincike za mu kai su kotu”, inji Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Usman Nagogo.

Kwamishin ‘yan sandan ya ce rundunar ta kama wani wanda ya tabbatar da cewa da hannunsa a kashe likitan.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan ’yan sanda sun lalata wani shirinsu na yin garkuwa da wani  mutum, sai dai har yanzu akwai wasu wadanda rundunar take nema ruwa a jallo.

Da ake gabatar da shi ga ‘yan jarida, wanda ake zargin ya ce wa ya kashe mutum akalla bakwai a hare-haren da suka kai a kan wani kauye a karamar hukumar Kaura Namoda.