✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke kasurgumin dan fashi a Bayelsa

Wanda ake zargin ya yi kaurin suna wajen aikata fashi da makami a jihar.

Jami’an rundunar ’yan sanda masu yaki da masu garkuwa da mutane a Jihar Bayelsa sun cafke wani kasurgumin dan fashi da makami, wanda yake cikin jerin sunayen ’yan fashi da makami da ake nema ruwa a jallo a Yenagoa da kewaye.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Asinim Butswat ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce an kama wanda ake nema ruwa a jallo, a wani samame da suka kai a hanyar Otiotio a Yenagoa, babban birnin jihar.

A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin hannunsa a wasu laifukan fashi da makami da ake bincike a kansu tare da abokansa, wadanda a halin yanzu suke hannunsu.

Ya ce: “Wanda ake zargin mai suna Keme Azorobor mai shekara 27, dan asalin Karamar Hukumar Bomadi, a Jihar Delta, wanda yake zaune a Yenagoa, an kama shi ne a wani samame da aka kai titin Otiotio, Yenagoa a ranar 24 ga watan Yuli 2022, da misalin karfe 11:45 na dare.

“An binciki wanda ake zargin kuma an samu wata bindiga kirar gida dauke da harsasai.

“Ana ci gaba da bincike don kama wadanda suke aiki tare don gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.