✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun cafke masu garkuwa 3 a jihar Delta

Bincike ya gano wanda ake zargin suna da hannu a sace wani mutu a ranar Lahadin da ta gabata.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta tabbatar da kame wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a yankin Agbarho na Karamar Hukumar Ughelli da ke Jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya ne ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya hakan a garin Warri a ranar Laraba.

“Da gaske ne rundunarmu ta cafke wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

“Amma an maida su baban sashen binciken manyan laifuka da ke hedikwatar ’yan sanda,” cewar Onovwakpoyeya.

NAN ta rawaito cewa an cafke wanda ake zargin ne a ranar Talata a yankin Agbarho da ke jihar.

Bincike ya gano suna da hannu a garkuwar wani mutum mai suna Emmanuel Piopio, ranar Lahadin da ta gabata.

An kama masu laifin a dajin Ophori-Agbarho tare da hadin gwuiwar sojoji da ’yan banga.