✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke mutum 259 kan zargin ta’addanci a Neja

’Yan sandan sun ce sun kama duka mutanen ne a watan Agusta.

’Yan sanda a Jihar Neja sun ce sun cafke kimanin mutum 259 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi ta’addanci, garkuwa da ma wasu manyan laifuka a Jihar.

Sauran laifukan da ake zargin mutanen da aikatawa sun hada da kisan kai da fyade da fadan manoma da makiyaya, dukkansu a watan Agusta.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Monday Kuryas ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Minna ranar Asabar cewa an aikata laifukan ne a Kananan Hukumomi 25 na Jihar.

“Mun gurfanar da mutum 119 daga cikin 259 din da muka kama a gaban kotu, 81 daga cikinsu kuma har yanzu suna fuskantar shari’a,” inji shi.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa akwai mutum 59 da har yanzu suke fuskantar bincike a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar, yayin da mutum tara kuma aka tura batunsu zuwa Ma’aikatar Shari’ar Jihar domin ta bayar da shawara kan matakin da ya fi dacewa da su.

Ya kuma ce jami’ansu sun sami nasarar kwato bindigu kirar gida kimanin guda tara daga hannun wadanda suka kama din.

Monday ya kuma ce rundunar ta dakile yunkurin kai hari a kauyen Mau’undu da ke Karamar Hukumar Mariga wanda wata matattara ce ta ’yan bindigar.

Daga nan sai ya ce sun umarci Turawan ’Yan Sandan yankunan Kananan Hukumomin Jihar da su kara sa’ido tare da tsaurara matakan tsaro a yankunansu.