✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke ’yan bangar siyasa 93 a Kano

'Yan sandan sun kama su yayin da ake tsaka da yakin neman zabe a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu ’yan bangar siyasa 93 kan zargin tada zaune-tsaye a lokacin yakin neman zabe a jihar. 

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mamman Dauda ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce matakin ya yi daidai da umarnin Babban Sufeton ’Yan Sanda, Usman Alkali, na tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a fadin kasar nan.

Ya ce jami’an rundunar sun kama mutum 53 da ake zargi a ranar 9 ga watan Fabrairu, a wani samame da suka kai Filin Wasa na Sani Abacha, da ke Kofar Mata.

Ya ce, sun kwato bindigogi biyu, wukake 32, gatari daya da kuma tarin layoyi, a yayin samamen.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ta kuma kama wasu mutum 40 da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci a cikin mako guda da ya gabata a fadin jihar.

Dauda ya ce: “Wannan na cikin wani aikin share fage da wata tawagar ‘Operation Restore Peace’ karkashin jagorancin CSP Bashir Gwadabe, jami’i mai kula da rundunar ’yan sanda da ke yakar ’yan daba suka gudanar

“Kayan da aka kwato sun hada da fakiti 62 na kwaya, kwalabe 60 na na maganin tari, wukake 28, babura hudu da keken dinki guda uku”.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Kwamishinan, ya ce kafin gudanar da ayyukan share fagen, Kwamitin tuntuba na hukumomin da ke kula da harkokin zabe (ICCES) ya gana tare da tantance shirye-shiryen da ake yi gabanin babban zaben da ke tafe.

Ya ce an samar da ingantattun na’urorin tsaro domin tabbatar da gaskiya da kuma samun nasara a babban zaben jihar.

Yayin da yake yaba wa hukumomin tsaro da kafafen yada labarai da al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke bayarwa, Dauda ya jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.