✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto dattijo mai shekara 80 da aka sace a Kano

An ceto Alhaji Nadabo a garin Chiromawa na Karamar Hukumar Garun Mallam.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta ceto wani dattijo dan shekara 80 mai suna Alhaji Nadabo da aka sace a garin Chiromawa da ke Karamar Hukumar Garun Mallam ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

DSP Kiyawa ya ce bayan samun rahoton sace mutumin ne rundunar ta dauki mataki cikin hanzari.

Ya ce, “muna samun rahoton ne Kwamishinan ’yan sanda na Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya tashi wata tawagar ’yan sanda ta Operation Puff Adder karkashin jagorancin CSP Usman Maisoro da umarnin kubutar da wanda abin ya shafa sannan su cafke wadanda suka aikata laifin.”

A cewarsa, matsin lambar da tawagar ’yan sandan ta yi wa masu garkuwa da mutanen ce ta sanya suka sako dattijon da suka sace.

“Tare da hadin gwiwar yan sa-kai da jamaar yankin aka samu nasarar ceto dattijon a wannan rana da aka sace shi kuma wadanda suka yi garkuwa da shi suka tsere.”

Kiyawa ya tabbatar da cewa, an tura karin tawagar Puff Adder yankin domin cafke wadanda suka aikata laifin.