✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun ceto mutum 15 daga hannun ’yan bindigar Zamfara

Maharan sun tsere bayan barin wuta da suma sha a hannun ’yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ceto mutum 15 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Gusau zuwa Funtuwa.

Kakakin rundunar, Muhammad Shehu, ya ce bayan samun labarin, rundunar tura ’yan sanda na musamman zuwa yankin inda aka gwabza kazamin fada, ’yan bindigar suka tsere zuwa cikin dajin, suka bar mutanen da suka sace.

“’Yan sandan sun garzaya cikin daji cikin gaggawa inda suka ceto mutum 15 da suka hada da mata bakwai, maza shida da yara biyu.

“An duba lafiyarsu yadda ya kamata, kuma sun yi magana da kwamishinan ’yan sanda don samun bayanan sirri.

“Za a sake hada su da ’yan uwansu nan ba da jimawa ba,” in ji Shehu.

A ranar Talata ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da mutanen zuwa cikin daji.

Jihar Zamfara dai na fuskantar hare-haren ’yan bindiga, sai dai jami’an tsaro na fatattaar su don dakile ayyukan bata-garin.