✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun ceto shugaban da aka sace a Kwara

Rundunar ta bayar da tabbacin za ta ceto ragowar da aka sace.

’Yan sanda sun ceto shugaban al’ummar Oluwalose, Alhaji Tunde Buhari, bayan ’yan bindiga sun sace shi a yankin Okolowo da ke Ilori, Jihar Kwara.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Okansanmi Ajayi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba inda ya ce, Buhari na daga cikin mutum biyu da ’yan bindigar suka sace.

Ajayi, ya kara da cewa an samu nasarar ceto mutumin ne bayan kokarin jami’an tsaro hadin guiwa a jihar.

A cewarsa, tuni rundunar ta mika mutumin ga iyalansa bayan duba lafiyarsa a asibiti.

Ajayi ya jadadda cewa rundunar na da karfin ceto ragowar mutanen da mahara suka sace.

“Kwamishinan ’yan sandan Kwara yana bai wa jama’a tabbacin ba su kariya.

“Kwamishina yana shawartar jama’a da su rika sanya ido sosai kan sha’anin tsaron kansu da kansu da kuma yanayin da ake ciki a unguwanni,” in ji shi.