✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto shugaban Jam’iyyar APC a Neja

’Yan sanda sun baza koma don cafke wadanda suka yi garkuwa da shi.

’Yan Sanda sun kubutar da shugaban jam’iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Kakakin ’yan sanda na jihar, DSP Wasiu Abiodun ne, ya sanar a ranar Asabar cewa an kubutar da dan siyasan ne a ranar Juma’a da misalin karfe 3:30 na yamma a kusa da dajin Igwama, gundumar Bobi ta Karamar Hukumar Mariga ta jihar.

  1. Cutar COVID-19 ta kashe mutum 11 a Najeriya
  2. Kwamishinan Neja ya sa masu garkuwa da shi zubar da hawaye

Abiodun ya ce, “An kubutar da wanda aka sace daga dajin, an bincike shi sannan aka kai shi Babban Asibitin Kontagora domin duba lafiyarsa, ana kuma ci gaba da kokarin gano masu laifin.

“An gano cewa a ranar 7 ga watan Agusta da misalin karfe 2:00 na dare, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan wanda aka kubutar da din tare da direbansa, Nasiru Bobi, a hanyarsu ta zuwa gona a kan hanyar Ukuru a cikin yankin Bobi na Karamar Hukumar Mariga.

“An harbi direban a kafa kuma maharan sun kyale shi, amma suka yi awon gaba da shugaban,” inji shi.

A cewarsa, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja ta tara jami’anta da sojoji da ’yan banga zuwa yankin domin farautar ’yan bindigar.

Ya ce daga baya an ceto direban an kai shi Babban Asibitin Kontagora, inda ya samu kulawar likita.

Kazalika, Abiodun ya nemi muhimman bayanai da za su taimaka wajen ceto daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke garin Tegina ba tare da wani abu ya same su ba.