✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun dakile fashi a Jihar Nasarawa

’Yan sandan sun kashe daga cikin ’yan fashin yayin da suka yi musayar wuta.

Rundunar Yan Sandan Jihar Nasarawa ta dakile wani farmaki da wasu yan fashi suka kai a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Bola Longe ne ya bayyana hakan.

Ya ce sun samu kira, inda aka sanar da su cewa bata-gari da ake zaton yan fashi ne sun tare titin Gidan Gambo, da ke kan hanyar Lafia-Shendam.

Ya kara da cewa daga nan aka aike da jamian yan sandan yankin Assakio, inda suka yi musayar wutar da yan fashin.

A yayin dauki ba dadin, yan sandan sun yi nasarar kashe daya daga cikin yan fashin wanda aka garzaya da shi asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Longe, ya ce an kwace adduna, wukake, da sauran makamai a hannun ’yan fashin, yayin da ragowar tsere cikin daji da raunuka.

A cewarsa jamian ‘yan sandan na ci gaba da sintiri a dajin domin gano maboyar ragowar da suka tsere.

Kwamishinan yan sandan ya gargadi masu aikata laifuka a jihar da su guji fadawa hannun rundunar, domin ba za ta raga musu ba.