✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Katsina

’Yan sandan sun dakile hare-hare guda biyu a yankin Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

’Yan sandan sun dakile hare-hare biyu na ’yan bindiga, inda suka kashe  kashe ’yan bindigar tare da ceto mutum takwas a Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce ’yan sandan sun dakile harin farko ne a kauyen Gandun Karfi da ke Karamar Hukumar Malumfashi, inda suka kashe dan bindiga daya sannan suka kwace bindiga kirar AK-47, babur kirar boxer, shanu 82 da tumaki 70.

“A ranar 17 ga watan Fabrairu 2022 da misalin karfe 12:40 na dare mun samu kiran agaji cewa ’yan bindiga sun kai farmaki kauyen Gandun Karfi a Karamar Hukumar Malumfashi, inda suka sace mata da dabobbi sannan suka nufi Karamar Hukumar Kankanra.

“Nan take Kwamishinan ’Yan Sanda ya jagoranci tawaga ta musamman da kansa, inda aka tare maharan a daidai Zurunkutum yayin da suke kokarin tsallakawa titin Kankara zuwa Sheme.

“Dakarun sun bude musu wuta kuma an yi nasarar kashe dan bindiga daya tare da ceto mata hudu ciki har da jarirai, bindiga AK-47, shanu 82 da tumaki 70.

“Kazalika, a wani lamari da ya faru a ranar Talata 15 ga watan Fabrairu 2022 da misalin karfe 6:50 na yamma, Baturen ’Yan Sanda na Kankara ya jagoranci tawagar ’yan sanda, inda aka yi dauki-ba-dadi da wasu ’yan bindiga da suka tare mutane a kan hanyar Kankara zuwa Zango, a nan ma an yi nasarar kashe dan bindiga daya daga tare da kwace babur kirar boxer,” cewar sanarwar.