’Yan sanda sun fara neman masu lalata da karnuka a Legas ruwa a jallo | Aminiya

’Yan sanda sun fara neman masu lalata da karnuka a Legas ruwa a jallo

    Sani Ibrahim Paki

Hukumomin ’yan sandan Najeriya sun sha alwashin kamawa, tsarewa da kuma hukunta masu karnukan da suke biyan mata don yin lalata da karnukansu a Jihar Legas.

Rundunar ta kuma ce jami’anta za su kama matan da suka yi lalata da karnukan don ya zama izina ga ’yan baya.

Kakakin Rundunar, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa, ya ce lamarin tsagwaron jahilci ne da ya cancanci hukunci a karkashin doka.

Ya ce, “Za mu dada matsa lamba wajen nema, bincike da kuma hukunta masu karnukan da aka kama suna ba mata kudi su yi lalata da karnukansu, da ma makamantan wadannan laifuffukan.

“Za kuma su amsa tambayoyi saboda laifin ya cancanci hukunci kuma abin Allah-wadai ne. Kwanan nan za mu kamo matan da sauran masu hannu a cikin irin wannan aikin jahilcin,” inji kakakin.

Binciken Aminiya ya gano cewa kundin manyan laifuka da na Penal Code sun tanadi hukuncin shekara 14 ga dukkan wanda aka kama da laifin yin lalata da dabbobi.

A kwanakin bayan ne bidiyon wata budurwa ya karade shafin sada zumunta na TikTok, inda take ikirarin cewa an biya ta Naira miliyan daya da rabi domin ta yi lalata da kare.

Rahotanni sun ce an dauki bidiyon ne a Jihar Legas, kuma mutane da dama sun yi ta mamakin dalilin da zai sa a biya mace makudan kudaden don kawai ta yi lalata da kare.