✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun gano idanun da aka kwakule wa yaro a Bauchi

An kama Isaac da Nensok da Yohanna bisa zargin aikata ta’asar

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta gano idanun Uzairu Salisu, yaron nan mai shekara 16 da aka kwakule wa idanu tare da cafke mutum uku da ake zargi da yin hakan.

Kakakin rundunar, DSP Mohammed Wakil ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a Bauchi ranar Litinin.

Ya ce wadanda ake zargin sun hada da Isaac Ezekiel mai shekara 32, mazaunin unguwar Rafin Zurfi da ke Yelwa a Bauchi da Nensok Bawa mai shekara 38, mazaunin gundumar Kabwir da ke Karamar Hukumar Kanke ta Jihar Filato da kuma Yohana Luka wanda aka fi sani Doctor Samu mai shekara 52 na yankin Golbong da ke gundumar Amper ita ma a Karamar Hukumar ta Kanke a Jihar Filato.

Wakil ya ce babban wanda ake tuhuma, Isaac Ezekiel ne da kansa ya amsa aikata laifin.

Ya ce, “Binciken da ’yan sanda suka yi a gidansa ya kai ga gano kwayar idanun yaron da wasu abubuwan da dama.

“Mun kuma gano kwayar idanun guda biyu da aka samu a cikin wata kwarya da kebur din da aka yi amfani da shi wajen aikata tabargazar sai kuma wata jaka da ke dauke da wasu magungunan gargajiya.

“Bincikenmu ya gano cewa wani lokaci a watan Afrilun 2022, babban wanda ake zargin, Isaac Ezekiel, ya hada baki da wasu mutum biyu wajen tattauna batun samo kwayar idanun mutum.

“A ranar 24 ga watan Yunin 2022, wajen misalin karfe 9:00 na safe ya yaudari wani mai suna Uzairu Salisu, mai kimanin shekara 16 mazaunin unguwar Jahun a birnin Bauchi, da nufin ya yi masa aiki a gona.

“Daga nan ne ya sa kebur ya daddaure shi har sai da ya fita daga hayyacinsa, sannan ya yi amfani da wuka ya cire masa idanun da nufin yin tsafi da su,” inji sanarwar ’yan sandan.