✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun gano ‘masana’antar jarirai’ a Ogun

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta gano da kuma tarwatsa wani gida na musamman da ake amfani da shi wajen haihuwar jarirai ana kuma sayar…

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta gano da kuma tarwatsa wani gida na musamman da ake amfani da shi wajen haihuwar jarirai ana kuma sayar da su kan N400,000.

‘Yan sandan sun gano cewa gidan wanda ke lamba hudu a kan titin Ibrahim Famuyiwa a Agbado da ke karamar hukumar Ifo, inda ake haihuwa da kuma sayar da jarirai bayan ajiye matan da aikinsu ke nan a ciki.

Karatan maza ne dai ke biyan kudi su kwanta da matan, wadanda da ba a  bayyana adadinsu ba, domin su dauki ciki su kuma haihu, sannan a sayar da jariran kan kudi Naira 400,000 a kowanne daya.

A wata sanarwa wacce Kakakin Rundunnar ‘Yan Sandan jihar, Abimbola Oyeyimi ya sanya wa hannu ta ce, jami’ansu sun kai samamen a gidan ne a ranar Litinin, a inda suka samu nasarar kame wasu mata su biyu.

Sanarwar ta ce, matan da aka kama, Christina D’ivoire Iyama da kuma Margaret Ogwu, ana zarginsu da tara matan da kuma gudanar da sana’ar amfani da gidan wajen samar da kuma sayar da jarirai.

Kakakin ya kuma ce sun sami nasarar kai samamen da kuma damke matan da ake zargi ne sakamakon wasu bayanan sirri da ofishin ‘yan sanda na yankin Ogbodo ya samu kan yadda matan biyu ke ajiye matan, da kuma biya a kwanta da su da kuma sayar da jarirai.

Christina D’ivoire ta furta cewa, ta sayar da irin wadannan jarirai da aka samar a gidan har guda uku daga matan da ke gidan daban-daban ga kwastominta.