✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun harbe dan fashi a Legas

Biyu daga ciki 'yan fashin sun tsere da raunin harbin bindiga.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas, ta ce ta yi nasarar kashe wani dan fashi a yankin Oshodi da ke jihar, a wani artabu da suka yi da gungun wasu ‘yan fashi.

Kakakin ‘yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), a ranar Alhamis.

Hundeyin, ya ce lamarin ya faru a ranar 24 ga watan Disamba, 2022 da misalin karfe 3 na dare a kan titin Akinpelu zuwa Oshodi a jihar.

Ya ce rundunar da ke yaki da ayyukan ‘yan fashi da ke caji ofis din Akinpelu, sun yi artabu da ‘yan fashin ne a lokacin da suke sintiri a wani shingen bincike.

Kakakin ya bayyana cewar ‘yan fashin sun bude wuta lokacin da suka hangi ‘yan sanda a kan hanyar, lamarin da ya sa jami’an da ke cikin shiri suka mayar da martani.

‘Yan sandan sun yi nasarar kashe daya daga cikin wadanda ake zargin yayin da biyu daga cikinsu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Sai dai ya ce rundunar na fadada bincike don gano inda wadanda suka tsere suka shiga, ya kuma roki jama’ar yankin da jami’an lafiya da su bayar da bayanan duk wanda suka gani da harbin bindiga.

Kakakin ya ce sun kwato karamar bindiga guda daya, janareta daya, komfuta guda 15 daga hannun wadanda ake zargin.