✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kafa rassa 5 don magance ta’addanci a Sakkwato

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kafa karin wasu rassa biyar da zummar inganta tsaro a  Jihar Sakkwato musamman wajen dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran…

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kafa karin wasu rassa biyar da zummar inganta tsaro a  Jihar Sakkwato musamman wajen dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka a fadin Jihar. 

Kakakin rundunar ’yan sandar Jihar, Mista Sanusi Abubakar ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata a birnin na Shehu.

Abubakar ya ce, rassan biyar wadanda za su kasance a karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’yan sandan Jihar, za su mayar da hankali ne a kan Kananan Hukumomin da ke gabashin Jihar da suka hada da Gwadabawa da Illela da Sabon Birni da Isa da kuma Wurno.

A cewarsa, a ranar Litinin ne rundunar ’yan sandan Jihar ta kaddamar da sabuwar rundunar ‘Operation PUFF ADDER II’, wadda za ta rika cikakken rangadi musanman a wuraren da ake zargin sun kasance tamkar matattar ta ’yan ta’adda a duk wani lungu da sako da ke fadin Jihar.

Kakakin ’yan sandan ya kuma bayyana cewa, rundunar ta kuduri samar da makamancin wadannan rundunoni a wasu Kananan Hukumomin Jihar biyar.

Idan ba a manta ba Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Litinin wasu ’yan bindiga suka kashe kimanin mutane 12 yayin da suka fita ceton wani attajirin dan kasuwa da aka sace a kauyen Amarawa da ke Karamar Hukumar Illela a Jihar ta Sakkwato.