✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama maharan da suka addabi Abuja da Nasarawa

An kwato muggan makamai a hannun gungun maharan.

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta cafke gungun wasu mutum 10 da ake zargin su da kai hare-hare a Abuja da Jihar Nasarawa.

Da yake gabatar da su a gaban manema labarai, Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Sadiq Abubakar, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wani otel da ke yankin Masaka, ’yan kilomitoci kadan zuwa Abuja.

An samu bindiga kirar AK-47 guda biyar, sai kwanson harsashi 22 da kuma kananan bindigogi guda uku a hannunsu.

Ragowar abubuwan da aka samu a wajensu sun hada mota kirar Toyota Camry 2000, katin aikin wani dan sanda da kuma janareto guda biyu.

Kazalika, rundunar ta cafke wasu bata-gari hudu da ake zargi da yin fashi da makami a unguwar Maitama da ke Abuja.

Har wa yau, wadanda ake zargin sun yi wa wani mai sana’ar POS fashin kudi.

An samu kananan bindigogi uku da harsashi 14, talabijin guda biyu, wayoyin hannu da kuma kayan yari da ake zargin fashin su suka yi.

Rundunar ta kuma gano maboyar wasu masu kai wa ’yan bindiga makamai ne.

A yayin bincike mutanen biyun da suka shiga hannun, sun bayyana cewa ’yan fashi da ’yan bindiga suke yi wa safarar makamai.

An samu harashi guda 900 da sauran muggan makamai a hannunsu wadanda ake kyautata zaton na ’yan bindiga ne.