✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama matashi da kullin Tabar Wiwi 250 a Kano

Matashin ya ce ya dauko Tabar ce daga Jiharsa ta haihuwa wato Edo zuwa Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani da take zargi da zama dilan miyagun kwayoyi dauke da kulli 250 na Tabar Wiwi.

Mutumin, mai suna Agbi Victor, mai shekara 33, an kama shi ne cikin wata koriyar mota kirar Honda yayin da rundunar tsaro ta Operation ‘Kan ka ce kwabo’ bisa jagorancin CSP Hassan Nasir Jega ke gudanar da sintiri a garin Kwanar Dangora da ke Karamar Hukumar Kiru a Jihar.

Da yake holen wanda ake zargin, jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce motar na dauke da kunshin wani busasshen ganye da ake zargin na Wiwi ne da ya kai na kimanin Naira miliyan daya da dubu dari bakwai da hamsin.

Da yake amsa tambayoyi, wanda ake zargin, ya amsa laifinsa da ake zarginsa, inda ya ce ya dauko kayan ne daga Jiharsa ta haihuwa wato Edo zuwa Kano domin kai wa ga wani Alhaji, inda jami’an tsaro suka cafke shi a kan iyakar Kano da Kaduna.

Rundunar ta ce yanzu haka ta fara farautar wanda za a kai wa Tabar bayan ya cika wandonsa da iska.

Kiyawa ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Kano Sama’ila Dikko ya ba da umarnin mika lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka da na binciken haramtattun kayen maye na rundunar, kuma za a ci gaba da tsare wanda ake zargin har sai an kammala bincike.