’Yan sandan kasar New Zealand sun kama wasu mutum biyu da ke yunkurin fasakwaurin gasassun kaji a cikin mota zuwa babban birnin kasar wato Auckland.
Birnin dai ya kasance cikin tsauraran matakan COVID-19 tun tsakiyar watan Agusta, inda aka hana kowa shiga ko fita daga yankin.
- Babban laifi ne mu gadar wa ’ya’ya da jikoki tarin bashi – Obasanjo
- Babu barazanar da za a yi mana kan ci gaba da mulki a 2023 – Dattawan Arewa
Kazalika, dukkan wasu sana’o’i da ba na wajibi ba, ciki har da na abincin gaggawa sun kasance a rufe.
To sai dai sauran sassan kasar na da karancin tsauraran matakan kariya daga cutar, yayin da shaguna da dama suka kasance a bude.
’Yan sanda sun ce jami’ansu da ke sintiri a hanyoyin da ke kan iyaka ne suka lura da wani motsi da basu amince da shi ba a wata mota rufaffiya da ke tafiya.
Daga yin arba da ’yan sandan, sai motar ta juya ta ranta a na kare, kamar yadda kakakin ’yan sandan kasar ya tabbatar a cikin wata sanarwa.
Sai dai daga bisani ’yan sandan sun gano cewa motar ta taso ne daga birnin Hamilton tana kokarin zuwa Auckland.
A cikin motar dai an gano kudi fiye da Dalar Amurka 70,207 da kuma kunshin gasassun kaji a ciki.
’Yan sandan dai sun ce ana sa ran za a gurfanar da mutanen a gaban kotu nan da ’yan kwanaki masu zuwa. (NAN)