✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama ‘yan fashi a Bayelsa

‘Yan sanda a jihar Bayelsa sun dakile ‘yan fashi a Karamar Hukmar Obia ta jihar Bayelsa, inda suka cafke wasu mutum uku suka kuma kwace…

‘Yan sanda a jihar Bayelsa sun dakile ‘yan fashi a Karamar Hukmar Obia ta jihar Bayelsa, inda suka cafke wasu mutum uku suka kuma kwace makamai.

Kakakin ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, a cikin wata sanarwa ya ce an damke mutanen ne da hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda ‘yan banga a yankin.

Ya ce, “an damke mutanen da aka tsare sun amsa laifin fashi da ake tuhumar su da aikatawa a garin Ogbia”.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bayelsa, Mike Okoli, ya gargadi masu aikata manyan laifuka a jihar da su shiga taitayinsu ko kuma su dandana kudarsu.

Ya ce, “an mika wadanda ake zargin ga Sashen Bincikin Manyan Laifuka na rundunar domin a yi cikakken bincike”.