‘Yan sanda sun kashe dan bindiga a Kaduna | Aminiya

‘Yan sanda sun kashe dan bindiga a Kaduna

‘Yan Sanda
‘Yan Sanda
    Bashir Isah

‘Yan sandan Jihar Kaduna sun ce sun kashe wani dan ta’adda daya kana sun karbe bindiga kirar AK49 daya da wata kirar gida guda daya.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma’a.

A cewar Jalige, bayan da suka samu kiran waya game da ‘yan bindigar da aka hango su a hanyar Galadimawa zuwa Kidandan da ke cikin Karamar Hukumar Giwa a jihar, daga nan aka tura jami’ai zuwa yankin don bin sawunsu.

Jami’in ya ce, “An yi zargin take-takensu na neman aiwatar da mugun halin da suka saba ne.

“Ganin haka ya sanya aka tura jami’an tsaro domin su dakile yunkurinsu da kuma bai wa yankin kariya.

“Jami’an sun yi nasarar fatattakar ’yan bindigar wanda hakan ya tilasta su tserewa cikin daji.

“Wasunsu sun ji rauni sakamakon alburshe su da aka yi, yayin da aka kashe daya tare da dauke bidigarsa kirarar AK49 da kuma babur dinsa,” inji jami’in.

Kazalika, ya ce rudunarsu tana bakin kokarinta wajen sauke nauyin da ya rataya a kanta na bai wa al’umma da dukiyarsu kariya.

(NAN)