✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

‘Yan sanda sun kashe dan fashi a Gombe

'Yan sandan sun yi artabu da 'yan fashi da makamin.

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kashe wani dan fashi da makami tare da raunata wasu da suka kai hari a hanyar Gombe zuwa Bauchi.

Lamarin dai na zuwa ne bayan da ’yan sandan suka samu rahoton cewa ‘yan fashin sun tare wata motar fasinja kirar bas da ta taso daga Bauchi zuwa Gombe.

Bayanai sun ce ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke kan hanyar garin Wuro-Dole a kan iyakar Gombe da Bauchi ne suka yi artabu da ’yan fashin.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya fitar a ranar Talata.

Ya ce direban bas din ya sanar da ’yan sandan cewar ’yan fashi sun tare hanya da Duwatsu suna kwace kudaden matafiya da kayayyakinsu.

ASP Mu’azu ya ce nan take suka shirya suka suka yi basaja a motar haya tare da fasinjoji su ma suka nufi wajen tare.

Ya ce bayan isar jami’an ne suka shiga artabu da ’yan fashin, wanda hakan ya kai ga nasarar kashe wani tare da raunata da dama daga cikinsu.

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan fashin na dauke da muggan makamai da suka hada bindiga kirar gida da sanduna da adda.

Sai dai kakakin ya ce babu wani da ya samu ko kwarzane daga bangaren ’yan sandan.

Ya kuma ce sun kai gawar wanda aka kashe Asibitin Kwararru na jihar, yayin da suke ci gaba da gudanar da bincike don gano inda sauran suka shiga.