✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kashe ’yan Boko Haram shida a Yobe

Yan tada kayar bayan sun kai hari tare da lalata wani bangare na ofishin ’yan sanda.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe hallaka ’yan Boko Haram shida da suka kai hari a garin Babbangida na Karamar Hukumar Tarmuwa.

Kakakin Rundunar, ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) aukuwar lamarin.

“Jami’anmu masu sintiri ne suka yi artabu da ’yan ta’adda bayan har suka kashe guda shida daga cikinsu, wasu kuma sun tsere da raunuka a jikinsu.

“Bayan ’yan ta’addan sun kai hari tare da lalata ofishin ’yan sanda da sansanin Soji, ’yan sanda sun yi musu kofar-rago”, a cewar shi.

Maharan sun lalata kayan gwamnatin jihar tare da sanya fargaba a zukatan mazauna yankin.