✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe ’yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Katsina

An aika da kasurguman ’yan bindigar da suka addabi jihar lahira kafin wayewar garin ranar Laraba

’Yan sanda sun kashe kasurguman ’yan bindiga biyu da jami’an tsaro suke nema ruwa a jallo a Jihar Katsina.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce jami’anta sun kashe ’yan bindigar ne kafin wayewar garin ranar Laraba, a lokacin da ’yan ta’addan suka kai hari da dare a Karamar Hukumar Dutsinma ta jihar.

“An aika kasurguman ’yan bindigar biyu, Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari lahira,” a cewar kakakin ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah.

Ya ce an kashe su ne lokacin da suka kai hari yankin Sakkwato Rima da ke Karamar Hukumar Dutsinma a jihar.

“A ranar 13 ga watan Disamba 2022 da misalin karfe 7:30 ja dare, mun samu kiran gaggawa cewa ’yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai hari yankin Sakkwato Rima da ke Karamar Hukumar Dutsinma da nufin sace mazauna yankin.

“Kwamandan ’yan sandan yankin da dakarunsa sun kai dauki, inda suka yi artabu da ’yan bindigar har suka yi nasarar kashe ’yan bindigar da aka dade ana nema ruwa a jallo,” a cewar Gambo Isah.

Ya kara da cewa an kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu da makamai masu yawa daga hannunsu miyagun.

Ana kuma ci gaba da gudanar da bincike a yankin da kewayensa don cafke sauran ’yan bindigar da suka tsere da raunin harbi a jikinsu.