✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 21, sun ceto mutum 206 a Kaduna

Kwamishinan ya ce rundunar na ci gaba da fadada tsaro a fadin jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Yekini Ayoku, ya ce rundunar ta ceto akalla mutum 206 tare da kashe mahara 21 a jiahr a shekarar 2022.

Kazalika, Kwamishinan ya ce rundunar ta kwato dabobbi 1,446 da aka sace a fadin jihar.

“Mun kwato harsasai 1,359 tare da babura 17 daga hannun ’yan bindiga da kuma buhu 15 na tabar wiwi,” in ji shi.

Ya bayyana haka ne a bayaninsa na karshen shekara ga manema labarai, inda ya ce sun kwato makamai sama da 49 daga hannun ’yan bindiga.

A cewar Yekini, mutum 780 ne suka shiga hannun rundunar bisa zargin aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ya ce rundunar na ci gaba da aiki tukuru don yaki da masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar.