✕ CLOSE Kiwon LafiyaRa’ayoyiRa'ayin AminiyaRahotoAminiyar KurmiHotunaGirke-GirkeSana'o'iKimiyya da Kere-Kere

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 7 a Neja

Kwamishinan 'yan sandan jihar, ya ce za a mika su ga kuliya don girbar abin da suka shuka.

’Yan sandan sun kashe ’yan bindiga bakwai a kauyen Kumbashi da ke Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.

Mista Ogundele Ayodeji, kwamishinan ’yan sandan jihar ne, ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Alhamis a Minna, babban birnin jihar.

“Mun samu rahoton harin da ‘yan bindigar suka kai kauyen Kumbashi, kuma nan take muka tattara jami’anmu domin daukar matakan tsaro cikin gaggawa,” in ji shi.

Ya ce rundunar ‘yan sanda da ‘yan banga da ke zaune a garin Kumbashi sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka kashe bakwai daga cikin maharan yayin da wasu suka tsere.

Ayodeji ya bayyana cewar wasu daga cikin ‘yan banga sun samu raunuka kuma an kai su Babban Asibitin Kontagora domin ba su kulawa.

Kazalika, rundunar ‘yan sandan ta kama wasu bata gari 17 da ake zarginsu da aikata laifuka a sassa daban-daban na kananan hukumomin Chanchaga da Bosso na jihar.

Ya ce, a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2022 wasu bata gari da ke kewayen Angwan-Daji da Limawa, sun yi artabu da muggan makamai, kuma a sakamakon haka aka kashe wani Ashiru Tofa mazaunin yankin Limawa.

Ayodeji ya ce, rundunar ‘yan sandan, ta samu nasarar cafke wasu mutane 17 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin Angwan-Daji da kuma Limawa.

Ya yi bayanin cewa, ‘yan sanda sun kama wani kasurgumin mai kwacen wayar hannu a yankin Limawa, wanda yake basaja a matsayin mai hawa babur mai kafa uku domin yi wa wadanda abin ya shafa fashin waya.

Ayodeji ya ce wanda ake zargin ya taimaka wa ‘yan sanda wajen kama wasu bata-gari guda 17 a sassa daban-daban na birnin.

“Abubuwan da aka gano a hannun wadanda ake zargin sun hada da almakashi guda uku, tukwanen tabar shisha guda biyu da kwalaben maganin tari guda bakwai da kuma fakitin sigari,” in ji shi.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a gaban kuliya.

Kwamishinan ‘yan sandan ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi maganin duk wasu da ake zargi da aikata miyagun laifuka kamar yadda doka ta tanada.