✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwato mutum 187 daga hannun ’yan bindigar Zamfara

An ceton mutanen da aka sace a kananan hukumomi uku a ranar Alhamis.

’Yan sanda a Jihar Zamfara sun ceto mutum 187 daga hannun ’yan bindiga a rana guda.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce mutanen da aka ceto sun hada da maza, mata da kananan yara daga kananan hukumomi uku.

  1. An ceto mutum 47 a gidan kangararru a Kano
  2. Mako biyar da sallamar Nanono, Buhari bai nada ministan noma ba

Ya ce, “Bayan aiwatar da sabbin matakan tsaro da Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauka, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro suna kai hare-hare kan maboyan ’yan bindiga a sassan jihar, don kawar da ’yan ta’adda da dangoginsu daga jihar.

“Yau (Alhamis) 7 ga Oktoba, 2021, ’yan sandan hadin gwiwa a Dajin Tsibiri da ke Karamar Hukumar Maradun, sun yi nasarar ceto mutum 187 da aka sace daga garuruwan Rini, Gora, Sabon Birni da Shinkafi na kananan hukumomin Bakura da Maradun da kuma Shinkafi”.

Sanarwar da ya fitar ta ce, “Wadanda aka sace din sun shafe makwanni da yawa a hannun masu garkuwar, kuma an kubutar da su ne ba tare da wani sharadi ba, bayan gagarumin aikin bincike da ceto na tsawon awanni”, in ji Shehu.

A ranar Alhamis din Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta mika wa gwamnatin jihar mutanen da aka ceto daga hannun ’yan binidgar.

Da yake mika wadanda aka ceto din ga Gwamna Bello Matawalle, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ayuba Elkanah, ya ce sabbin matakan tsaron da aka sanya a jihar na samun gagarumar nasara, ta ta kai ga kubutar da daruruwan wadanda aka sace.

A cewarsa ’yan bindiga da dama sun shiga hannu tare masu hada baki da su, kuma an gurfanar da wasu a gaban kotu, wasu kuma ana kan gudanar da bincike a kansu.

Elkanah ya ba da tabbacin cewa ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da yin iya bakin kokarinsu don tabbatar da dawowar dawwamammen zaman lafiya da tsaro a Jihar Zamfara.

Da yake mayar da jawabi, Matawalle ya godewa ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro saboda jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da sabbin matakan tsaro a jihar.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya wakilta, ya ba da tabbacin kara ba da goyon baya ga hukumomin tsaro a jihar, don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.