✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwato mutum 8 daga masu garkuwa a Kaduna

’Yan sanda sun yi nasarar kwato mutu takwas da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su a Jihar Kaduna. ’Yan sandan sun…

’Yan sanda sun yi nasarar kwato mutu takwas da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su a Jihar Kaduna.

’Yan sandan sun kuma kwato bindiga kirar AK-49 daga hannun bata-garin da halin yanzu ake neman su gadan-gadan.

Mutanen da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su fasinjojin wata moat ce da aka tare kan hanyar Zariya zuwa Kaduna a hanyarta da wucewa zuwa Jihar Delta a ranar 29 ga Fabrairu, 2021.

Kakakin ’yan sanda a Jihar  Kaduna, Mohammed Jalige ya ce jami’an Rundunar Operation Puff Adder II ne suka kubutar da mutanen a yayin da suke sintiri a yankin Galidamawa/Kidandan  na Karamar Hukumar Giwa ta Jihar.

“Da ganin jami’an Rundunar, sai masu garkuwar suka tsere suka bar wadanda suka yi garkuwa da su da bindiga kirar AK-49 guda daya; A nan ne aka ceto mutum takwas ba tare an yi musu lahani ba,” kuma wadanda aka kubutar din ne suka bayyana cewa garkuwa da su aka yi.

Ya ce mutanen da aka kubutar sun hada da “Bala Ibrahim, Ede Gloria daga Jihar Ebonyi, Japheth Sani daga Jihar Kebbi, Kinsley Edgbue daga Jihar Delta, Anthony Okafor da Gabriel Agu da kuma Chibuzo Nwokorie daga Jihar Anambra da kuma Ifenyi Samuel dan Jiha Enugu.”

Jalige ya ce an kai wadanda aka kubutar din asibiti inda ake duba lafiyarsu kafin a mika su ga danginsu.

Rundunar, a cewarsa, na ci gaba bin sawun ’yan bindigar da suka tsere domin tabbatar da ganin sun girbin a bin da suka shuka.