✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Legas

’Yan sanda sun tarwatsa taron masu zanga-zanga daga jam’iyyar siyasa ta SPN, da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta soke. Akalla mutum 15 ne ’yan…

’Yan sanda sun tarwatsa taron masu zanga-zanga daga jam’iyyar siyasa ta SPN, da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta soke.

Akalla mutum 15 ne ’yan sandan suka kama, a lokacin taron zanga-zangar da ’yan rusasshiyar jam’iyyar suka gudanar ranar Alhamis a Jihar Legas.

Mutanen na zanga-zangar soke jam’iyyar SPN da INEC ta yi ne sabanin umarnin Kotun Daukaka kara; suna kuma kira da a soke karin farashin man fetur da wutar lantarki da aka yi a Najeriya

’Yan jam’iyyar sun fara tattakin ne daga Sakatariyar Kungiyar Kwadago ta NLC da ke Yaba, kafin ’yan sanda su tarwatsa su a Ojuelebga inda aka tsare wasu daga cikinsu.