✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda za su fara dirar mikiya a kan masu karya dokokin kariyar COVID-19

An kuma umarci Kwamishinonin rundunar a jihohi 36 da Abuja da su ma su yi hakan.

Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya umarci manyan jami’an rundunar dake kula da shiyyoyi 17 na kasar nan da su fara aikin tabbatar da ana bin Dokokin Kariya Daga COVID-19 na 2021 yadda ya kamata.

Ya kuma umarci Kwamishinonin rundunar a jihohi 36 da ma Babban Birnin Tarayya Abuja da su ma su yi hakan.

Babban Sufeton, a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar na kasa, Frank Mba ya fitar ranar Litinin, ya ce jami’ansu za su tabbatar jama’a na bin matakan sau da kafa.

Sai dai ya gargadi jami’an rundunar da su kiyaye da hakkokin mutane yayin gudanar da aikin tursasawar, inda ya yi kira ga jama’a da su rika bin dokar wacce Shugaban Kasa ya sanya wa hannu a makon da ya gabata a radin kansu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Daukar matakin ya biyo bayan amincewa da Dokokin Kariya Daga COVID-19 na 2021 wanda ya tilasta wa Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa da sauran jami’an tsaron da aka ayyana a cikinta kan su tabbatar ana bin matakan a wuraren taruwar jama’a kamar wuraren ibada, makarantu, bankuna, ababen hawa na haya, otal-otal, gidajen yari, hana cunkoson jama’a da kuma yin amfani da takunkumi.

“Babban Sufeton na kira ga jama’a cewa zuwan annobar ya kawo karin dawainiya gare su, yana mai yin kira ga ’yan kasa da su bi dokokin domin kariyar kowa da kowa,” inji sanarwar.

Sabuwar dokar da Shugaba Buhari ya sanya wa hannu dai ta tanadi hukuncin daurin watanni shida ko biyan tara ga duk wanda aka kama yana karya dokar, musamman ta bangaren amfani da takunkumi.