✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Sintiri sun kama masu ba ’yan ta’adda bayanai a Zariya

Sun shiga hannu bayan sun kashe mutane sun kuma yi garkuwa da matan aure a Zariya.

Kungiyar ’Yan Sintiri a Zariya ta Jihar Kaduna ta damke wasu mutum uku da ake zargin su ke ba masu garkuwa da mutane da kuma ’yan ta’adda bayanai.

An dai cafke su ne a yankin Dutsen-Abba ta Karamar hukumar ta Zariya.

Wadanda aka kama sun hada da Mu’azu Sani wanda kanin Kansilan da aka dauki matarsa ne a kwanakin baya, sai Mubarak Adamu mai shekaru 20 da ke Anguwar Makada da Faisal, mazaunin Unguwar Malam Atiku duka a gundumar ta Dutsen Abba.

A ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 da misalin karfe 11 na dare ’yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK 47 suka afka wa kauyen Unguwan Hazo da ke Dutsen Abba.

A lokacin dai sun kashe wani mai suna Musa Isa dan shekara 28 da haihuwa da Yusuf Sulaiman mai shekara 30, yayin da aka harbi matan aure biyu wanda yanzu haka suke kwance a asibitin kauran Wali a Zariya.

Maharan sun kai hari ne kauyen domin kwace babura kirar Boxer guda hudu daga a gidan wani kansila mai wakiltar gundumar Dutsen Abba, mai suna Abdulaziz Sani, a kauyen Anguwar Makada.

Wadanda aka sace din sun hada da matar kansilan mai suna Samira da wata matar aure mai suna Halima.

Sai dai kungiyar sintiri ta Jihar Kaduna da ke Unguwar Mai Turmi a Karamar Hukumar Igabi sun tare masu garkuwan inda suka samu nasarar ceto wadanda aka sace, da kuma kwato baburan.