✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan siyasa da masu kada kuri’a ne barazanar Zaben 2023 —Jega

Burinsu kawai shi ne su yi nasara ta ko wane hali.

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce ’yan siyasa da ma masu zabe su ne babbar barazana ga nasarar zabukan da ke tafe na ranar 25 ga watan nan na Fabrairu da kuma na 11 ga watan Maris.

Ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatar da babban jawabi jiya Talata a Abuja, a wurin taron wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman tare da hakuri da juna da kuma yin zabe cikin kwanciyar hankali da ba tare da wata matsala ba, wanda Cibiyar Da’awa da Tabbatar da Jin Dadin Jama’a ta Babban Masallacin Tarayya da ke Abuja ta shirya.

Farfesan ya ce wadanda ke kiran kansu ‘yan siyasa, da suka hada da masu takara su ne rukunin masu ruwa da tsaki a harkar da kusan za a iya cewa ba a ga wani sauyi na kirki a kan yadda suke gudanar da al’amuransu da suka danganci zabe ba tun 1999.

“Burinsu kawai shi ne su yi nasara ta ko wane hali, inda suke daukar zabe a matsayin wani abu na ko a mutu ko a yi rai.

“Kamar yadda suke yi tun 1999, suna ci gaba da yin haka, kuma za su iya yin hakan a 2023,” in ji shi.

Jega ya kara da cewa; “Yadda ba a hukunta su kan abin da suke yi, haka kuma suke kara dilmiya cikin magudi da miyagun abubun da suke yi.

“Wanda wannan ka iya zama babban kalubale ga zabukan 2023.”