✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan siyasa sun bullo da sabon salon sayen katin zabe —INEC

INEC ta zargi ’yan siyasa da ba wa mutane kudi su dauki lambar katin zabensu

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta zargi ’yan siyasa da bullo da sabon salon sayen katin zabe na dindindin a hannun ’yan Najeriya, inda suke ba su kudi su dauki Lambar Shaidar Katin Zaben (VIN).

Mukaddashin Kwamishinan INEC na Kasa mai kula da jihohin Nasarawa, Kaduna da Filato da Yankin Birnin Tarayya, Mohammed Haruna, ya bayyana cewa a halin yanzu mutum biyu sun shiga hannu a jihohin Kano da Sakkwato.

“Mun san cewa ’yan siyasa na sayen katin zabe na dindindin a hannun mutane, alhali duk wanda ya sayar da nasa, ko ya ba wa wani, to shi ma ya aikaita laifi a karkashin Dokar Zabe.

“Wasu za su iya tuna cewa INEC ta gurfanar da wasu mutum biyu kuma kotu ta kama mutanen da laifin mallakar katunan zabe ta haramtacciyar hanya.

“Don haka ina rokon jama’a su fito su karbi katin zabensu na dindindin, su adana, kuma su tabbata a ranar zabe sun je sun kada kuri’arsu, domin duk wanda ba shi da katin zabe na dindindin ba zai kada kuri’a ba.”

Muhammad Haruna ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da shirin #YourVoteMatters da wata kungiyar sanya ido kan zabe mai suna NESSACTION ta yi a Abuja ranar Litinin.

Shugabar NESSACTION, Eniola Cole, ta ce shirin nasu zai raba abin hasafi da nufin ba wa mutane kwarin gwiwar fita su karbi katin zabensu na dindinin a al’ummomin Yankin Babban Birnin Tarayya da kuma jihohin Nasarawa da Filato.

Manufar, a cewarta, ita ce ba wa INEC gudunmawa domin a samu karin mutanen da za su fita su karbi katin zabensu na dindinin kafin lokacin zaben 2023, da kuma ba wa mutane kwarin gwiwar fita su jefa kuri’arsu a ranar zabe.

Cole ta yi kira ga jama’a da su “yi amfani da lokacin da INEC ta sanar su karbi katin zabensu na dindidin daga ranar 12 ga Disamba, 2022 zuwa 22 ga Janairu, 2023 a wuraren da hukumar ta sanar.”

INEC at sanya ranar 12 ga Disamba, 2022 zuwa 5 ga Janairu, 2023 a matsayin lokacin karbar katin zabe of cibiyoyin zabe gundumomi 8,809 da ke fadin Najeriya, har da ranakun karshen mako.

Daga ranar 6 zuwa 22 ga Janairun 2023 kuma, rabon zai koma ofisoshin hukumar na kananan hukumomi.