✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda 13,243 da iyalansu sun mika wuya a Arewa maso Gabas – Sojoji

Hedkwatar ta ce adadin ya kunshi maza da mata da kuma kananan yara.

Hedkwatar Tsaro ta Kasa ta ce kimanin ’yan ta’adda 13,243 tare da iyalansu ne suka mika wuya ga sojoji a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Mai rikon mukamin Daraktan yada labarai na hedkwatar, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan, lokacin da yake bayar da karin haske kan ayyukan sojojin a fadin Najeriya ranar Alhamis a Abuja.

A cewarsa, ’yan ta’addan wadanda suka mika wuyan sun hada da maza 3,243, mata 3,868  da kuma kananan yara 6,234.

Ya ce dakarun rundunar tsaro ta Operatin Hadin Kai sun kaddamar da munanan hare-hare a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya ce sun sami gagarumar nasara a cikin makonni biyun da suka gabata.

Ya ce jerin hare-haren wadanda aka kai ta sama da kasa a sassa da daban-daban na yankin sun yi matukar kassara ayyukan ’yan ta’addan, da yawa daga cikinsu kuma sun mutu.

Bernard ya ce sun kuma kama masu samar musu da bayanai da masu kai musu kayayyaki da dama, yayin da wasu kuma suka ajiye makamansu sannan suka mika wuya ga sojoji.

Ya ce, “Wasu daga cikin nasarorin da muka samu sun hada da a hanyar Gwoza zuwa Yamtake zuwa Bita, hanyar Gwoza zuwa Farm Centre zuwa Yamtake da tsaunin Mandara da kuma garuruwan Pulka da Hambagda, dukkansu a Jihar Borno.

‘A jimlace, mun hallaka ’yan ta’adda 29, mutum 13 da ke samar da bayanai da kayan aiki kuma sun shiga hannu yayin hare-haren,” inji shi. (NAN)