✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun guntule wa mutum hannu, sun sace shanu 300 a Zamfara

Maharan sun far wa garin Bukkuyun ne suna harbe-harbe, suka rika bi gida-gida suna yin awon gaba da shanu da kuma mutane

’Yan bindiga sun guntule wa wani mutum hannu sannan suka sace shanu akalla 300 ranar Juma’a a  Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.

Shaidu sun ce zugar maharan sun far wa garin Bukkuyun ne suna harbe-harbe, suka rika bi gida-gida suna yin awon gaba da shanu da kuma mutane.

Wani dan garin mai suna Babangida ya ce, “Sun yi awon gaba da mutane da dama, harin jami’an tsaro ya sa suka arce zuwa cikin daji.

“Ba a cika kawo wa garin Bukkuyum hari ba, amma mutanen yawancin kauyukan da ke yankin sun yi kaura saboda yawan hare-haren ta’addanci.

Mutumin da aka guntule wa hannu a harin Bukkuyum
Mutumin da aka guntule wa hannu a harin Bukkuyum, kwance a asibiti. (Hoto: Shehu Umar).

“Wadansu mutane da suka gudo daga kauyukansu zuwa nan ma na daga cikin wadanda ’yan ta’addan suka yi awon gaba da dabbobinsu.

“Maharan sun kuma shiga gida wani mai suna Inno, suka guntule hannunsa; an garzaya da shi asibiti, sai yanzu ya farfado bayan ya jima bai san inda yake ba.

“Wasu mutum biyu kuma da suka samu raunin harbi suna samun sauki, har yanzu muna kokarin gano iya barnar da suka yi mana,” in ji Babangida.

Bata-garin sun yi wannan aika-aika a garin Bukkuyum ne sa’o’i kadan bayan Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da dokar hana fita a kananan hukumomomin Bukkuyum da Anka da Gummi.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, amma ya kasa samun sa a waya, har aka kammala hada wannan rahoton.

A baya-bayan nan, an samu karuwar hare haren ’yan bindiga a yankin Bukkuyum, wanda ya sa mazauna  da dama yin kaura.

A ranar Laraba ta makon jiya, wasu mutum kimanin 20 suka rasu sakamakon kifewar kwale-kwalen da suka hau domin tsere wa harin ’yan ta’adda a yankin.