✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun hallaka matafiya 18 a Nijar

Fararen hula akalla 18 ne masu tayar da kayar baya suka yi wa kisan gilla a yankin Tillaberi da ke Yammacin kasar Jamhuriyar Nijar.  …

Fararen hula akalla 18 ne masu tayar da kayar baya suka yi wa kisan gilla a yankin Tillaberi da ke Yammacin kasar Jamhuriyar Nijar.
 
Hukumomin kasar sun ce mutanen da maharan suka kashe matafiya ne a cikin wata babbar mota da maharan suka tare a yankin Tillaberi da ke Yammacin kasar.
 
Rahotanni daga yankin na Tillaberi sun ce ‘yan ta’addar da suka kai harin a bisa babura sun tare motar da mafafiyan suke ciki ce a tsakanin wasu kauyuka yankin na Tillaberi.
 
Yankin Yammacin Jamhuriyar Nijar ya yi shekaru yana fama da hare-haren ta’addanci daga mayakan Jihadi wadanda suka addabi yankunan kasashen Mali da Burkina Faso masu makwabtaka da Nijar a yankin.
 
A halin yanzu dai kasashen Mali da Burkina Faso sun koma karkashin mulkin soji, bayan sojojin kasar sun hambarar da gwamnatocin ‘yan siyasa bisa zargin shugabannin siyasa da gazawa wajen magance matsalar hare-haren ta’addanci.