✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda za su kai hare-hare a lokacin Kirsimeti —DSS

Za su yi kai hari da abubuwan fashewa a wuraren taruwar jama’a a lokacin bukukuwa

Hukumar tsaro ta DSS ta bankado shirye-shirye bata-gari na kai hare-hare a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a Najeriya.

DSS ta ce ta samu rahoton shirin miyagun na amfani da abubuwan fashewa da wasu muggan makamai don kai hare-haren a wuraren tauwar jama’a da wasu wuraren masu rauni domin sanya tsoro a zukatan al’umma.

“Saboda haka ake rokon jama’a da su kasance masu lura sosai su kuma kai wa jami’an tsaro rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba”, inji hukumar ta DSS.

Sanarwar hukumar ya kara da cewa: “Hukumar na aiki da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dukiyoyi”.

Hukumar ta yi wa masu neman tayar da hankalin jama’a kashedi cewa za su yaba wa aya zaki.

Ta kuma tabbatar da shirinta na ba da cikakken tsaron rayuka da dukiyoyin a lokacin bukukuwan karshen shekara da ma bayan nan.

“Mun samar da lambobin kar-ta-kwana: 08132222105 da 09030002189 da shafin tuntubar mu kai tsaye www.dss.gov.ng.

“Muna shawartar jama’a su yi amfani da wadannan kafafen da dangoginsu na sauran hukumomin tsaro domin ba da rahotanni a kan lokaci”, inji kakakin DSS, Peter Afunanya.

Ya kuma gargadi masu neman tayar da zaune tsaye da su sauya tunani tun kafin dubunsu ta cika su dandana kudarsu.

Afunanya ya ce hukumomin tsaro sun tashi haikan domin kare al’ummar Najeriya.