✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan takarar Gwamnan Kano sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya

An gudanar da zaben ne a Kano ranar Laraba

’Yan takarkar kujerar Gwamnan Jihar Kano a karkashin jam’iyyu daban-daban sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin da babban zaben 2023 yake dada karatowa.

Kwamitin Zaman Lafiya na Jihar Kano (KPC)  da hadin gwiwar Cibiyar Kukah da Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa ne ya gayyaci ‘yan takarar domin sanya hannun ranar Laraba.

Taron dai an shirya shi ne domin fadakar da ‘yan takarar muhimmacin zaman lafiya kafin da lokaci da kuma bayan kammala zaben.

Har ila yau, kwamitin ya  ja hankalin matasa da ke amfani da kafafen sada zumunta da su zamo masu yada abin da zai amfanar da jama’a da kuma kawo zaman lafiya a fadin Najeriya.

Yanzu haka dai ‘yan takarar sun sanya hannu a kan takaddar tabbatar da zaman lafiyar, yayin gudanar da zaben dama kuma bayansa.

Daga cikin ‘yan takarar kujerar  Gwamnan da suka sanya hannu a taron sun hada da Salihu Tanko Yakasai na Jam’iyar PRP da Sha’aban Ibrahim Sharada daga Jam’iyar ADP da  Injiniya Abba Kabir Yusuf na Jam’iyar NNPP,

Sai kuma mataimakin dan takarar Gwamnan jahar Kano na Jam’iyar APC Murtala Sule Garo da Bashir I. Bashir na Jam’iyar LP.

Sauran su ne Muhammad Abacha na Jam’iyar PDP da kuma Mallam Ibrahim Khalil na Jam’iyyar ADC wanda Mataimakinsa na ADC ya wakilta. Sai kuma Bala Gwagwarwa daga Jam’iyar SDP.

Wakiliya a Majilisar Dinkin Duniya da ma Afirka gaba daya, Uwargida Giovanie Biha ta ja hankalin ‘yan takarar da su tabbatar da an gudabar da zaben na 2023 cikin lumana.